
Shugaban Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC), Aminu Maida ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin rage wahalhalu ga ‘yan Najeriya.
A watan Yulin shekarar 2023 ne, Shugaba Tinubu, ya fara dakatar da harajin amma Majalisar Dokokin kasar ta sake dawo da batun a shekarar 2024 domin samar da Ζarin kuΙaΙen shiga, kafin daga bisani a yanzu ya soke shi gaba daya.

