
Shugaba Tinubu Ya Nemi A Kawar da Makaman Nukiliya Gaba ɗaya
Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira da a kawar da makaman nukiliya a duniya gaba ɗaya, yana mai cewa hakan ne kawai zai tabbatar da tsaron bil’adama daga barazanar amfani da su ko fashewarsu ba da gangan ba.
Tinubu ya yi wannan kira ne a jawabin da aka gabatar da sunansa a babban taron tunawa da Ranar Kawar da Makaman Nukiliya a hedkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York. Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ne ya wakilce shi a wajen taron.
Shugaban ya jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da taka rawar gani wajen tabbatar da cewa an kawar da makaman nukiliya gaba ɗaya. Ya yi gargadi ga ƙasashen da ke da waɗannan makamai da su tuna illolin da ka iya biyo baya ga lafiyar ɗan adam, muhalli da tattalin arziki idan aka yi amfani da su.
Tinubu ya bayyana damuwarsa kan yadda ƙasashen da ke da makaman nukiliya ke nuna jinkiri da son zuciya wajen aiwatar da matakan da aka amince da su domin kawar da makaman. Ya yi kira ga ƙasashen su daina gwaji, ci gaba da ƙerawa ko sabunta makaman nukiliya.
Shugaban ya kuma yi nuni da yarjejeniyar Pelindaba da ƙasashen Afirka suka amince da ita wadda ta haramta makaman nukiliya a nahiyar, yana mai cewa sauran yankuna na duniya ma ya dace su bi sahu.
Ya ce Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa sun rungumi amfani da fasahar nukiliya ta fuskar zaman lafiya domin bunƙasa ci gaba, tare da kira ga ƙasashe su kiyaye dokokin tsaro da hana yaduwar makaman nukiliya.
A ƙarshe, Tinubu ya jaddada cewa amfanin kawar da makaman nukiliya ya fi girma, yana mai kira ga ƙasashe su nuna gaskiya da jajircewa domin ganin an kai ga duniya marar makaman nukiliya.

