
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja a yau Lahadi domin halartar taron shugabannin ƙasashe na “Aqaba Process” a birnin Rome na ƙasar Italiya.
Taron, wanda zai fara a ranar 14 ga watan Oktoba, zai mayar da hankali kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin Yammacin Afirka.
An kaddamar da Aqaba Process a shekarar 2015 karkashin jagorancin Sarkin Jordan, Abdullah II, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Italiya. Manufarsa ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe da hukumomin tsaro wajen yaki da ta’addanci da sauran manyan barazanar tsaro.
A cewar fadar shugaban ƙasa, tattaunawar za ta mai da hankali kan yadda za a magance yaɗuwar ƙungiyoyin ta’addanci a Sahel, da haɗin gwiwar da masu laifi ke yi da ‘yan ta’adda, da kuma barazanar ta’addanci da fashi a teku da ke ƙara taɓarɓarewa a Tekun Guinea.
Za a kuma tattauna yadda za a yaki yaɗa ra’ayin ƙungiyoyin ta’addanci a intanet da kuma yadda za a katse hanyoyin sadarwar da suke amfani da su wajen yaɗa saƙonni da kuma jan magoya baya.
Shugaba Tinubu zai yi wasu tattaunawa na kashin kai da shugabannin ƙasashe daban-daban domin neman hanyoyin magance kalubalen tsaro da suka addabi yankin.
Shugaban ya samu rakiya daga wasu manyan jami’an gwamnati ciki har da Ƙaramar Ministan Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar, Mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da kuma Darakta-Janar na Hukumar Sirri ta Kasa (NIA), Mohammed Mohammed.

