
SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO YA BAYYANA FARIN CIKINSA DA SAMUN MAHADDATA ALQUR’ANI GUDA 20 A MAKARANTAR MURTALA ISLAMIYYA DORAYI
Mai Martaba Sarkin ya bayyana farin cikinsa tareda da godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya baiwa daliban damar sauke Alqur’ani da Kuma haddaceshi.
Sarkin yayi wannan bayani ne a lokacin da Iyaye da Malamai da Dalibai na Makarantar Madarasatul Murtala Islamiyya Dorayi suka ziyarceshi a fadarsa dake Gidan Nassarawa a Birnin Kano, Najeriya.
A don haka ne ma Sarkin ya godewa Malaman wannan Makaranta tareda yi musu addu’a Inda ya bukaci daliban su cigaba da zurfafa neman iliminsu Domin amfanar da sauran al’uma baki daya.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya Kuma basu tabbacin dukkan Hadin kan masarautar ta Kano akan dukkan bukatun da suka bijiro dasu.
A gefe guda kuwa da yake nasa Uba ga Makarantar Kuma Shugaban Cibiyar bayar da Magani ta addinin Musulunci Dr. Abdullahi Idris Dan Fodio Dorayi yace sun Kai ziyarar ne Domin girmamawa tareda neman albarka daga Mai Martaba Sarkin.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

