
Mai Martaba Sarkin Kano ya bukaci hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin kungiyoyi daban daban a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace yana sane da dukkan abubuwan da suke gudanarwa domin cigaban al’uma.
Ya godewa Yan Kungiyar tareda bukatar su rubanya addu’oi da ayyukan Kungiyar.
Yace bayan kokarin da shugabanni keyi al’uma suna gudunmawar da zasu bayar ta hanyar yin addu’oi domin samun warwarewar tabarbarewar al’amuran rayuwa.
Yayi fatan yadda Kungiyar ta dakko ayyukan ta Zasu cigaba dayin hakan Domin samun Nasarar da ake bukata.
Tunda farko da yake jawabi Shugaban Kungiyar Malam Hamza Umar yace sunzo fadar Sarkin Kano ne domin neman tubari tareda sa albarka a Kungiyar tasu.
Mai Martaba Sarkin ya sake karbar bakuncin kungiyar Hadin kan Matasa ta kasa bisa Jagorancin Ustaz Muhd, Yana Mai cewa sunzo ne domin ziyarar ban girma da Kuma sanarwa da Mai Martaba Sarki irin ayyukan da Kungiyar takeyi.S
a Hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa Sakataren Yada labarai na Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL. 3/09/2025
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

