
Madarasatul Saadatul Dharaini tai bikin saukar karatu alkurani maitsarki na Dalibai 22 a ranar Lahadi 5th October. 2025
Angudanar da bikin saukar ne a harabar makarantar Unguwar kawaji karkashin Jagorancin sakataren makarantar Mal. Suleiman Isyaku Dakata
Bikin saukar Karatun Alkurani Maigirma yasamu Jagorancin darasun daga fitaccen Babban Masanin kuma mahaddaci Goni Dr. Faruk Umar dayayiwa dalibai yakuma bayyana janhankali ga iyayi sucigabada namijin kokarin ganin yara masu tasowa sun riko da Alkurani da sunna manzon tsira Annabi Muhammadu Rasoulillah
Malama Aisha Muhammad Maihula itace shugabar makaranta ta bayyana farincikinta na samuwar wanann dama da matan aure da matasa suka samu nacewa suyi kokari su riko da abun da suka koya na tsawon lokaci wanda zai anfani rayuwarsu da ta duk Musulmi
Iyaye da dalibai sunyi murna kwarai da gaske ganin irin yacce suke cike da farinciki

