
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta gurfanar da wani matashi mai suna Naziru Mik’ailu a gaban kotun shari’ar Musulunci da ke unguwar Danbare, bisa zargin yunkurin kashe mahaifinsa.
Rahoton ya bayyana cewa zaman kotun ya gudana ne a ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025, inda aka gabatar da ƙarar gaban mai shari’a Munzali Idris Gwadabe.
A cewar mahaifin matashin, rikici ya barke tsakaninsa da ɗansa a unguwar Rimin Auzinawa, lamarin da ya kai ga Naziru ɗaukar wuƙa da nufin caka masa.
Sai dai a nasa bangaren, Naziru ya musanta zargin, inda ya ce abin da ya faru ba komai ba ne illa ƙaramin sabani tsakaninsa da mahaifinsa.
Bayan sauraron bayanai daga ɓangarorin biyu, mai shari’a Munzali Idris Gwadabe ya bayar da umarnin a tsare Naziru Mik’ailu a gidan yari, har zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Domin neman Karin bayani ko saka a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027314462 ko abknaisa100@yahoo.com

