
Hukumar tace Fina-finai a Kano ta gayyaci waɗanda suka gudanar da muƙabala da su gaggauta miƙa kansu ƙasa da sa’o’i 24
Hukumar tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta Haramta shirya dukanin wata muhawara a tsakanin mawakan addini, tare da gayyatar mai yabon nan Usman Maidubun Isa, da Shehi Mai Tajul’izzi, da sauran waɗanda suka jagoranci muhawarar tasu, da su bayyana a gabanta a ƙasa da awanni 24.
Wannan na cikin sanarwar da jami’in yaɗa labarai na hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano, Abdullahi Sani Sulaiman, ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Talata 16 ga watan Satumban 2025.
Sanarwar ta ce, shugaban Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i a jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya sanar da haramta duk wata nauyin muhawara daga mawakan addini a faɗin Jihar Kano, ba tare da izinin hukumar ba.
Ya ce an ɗauki wannan mataki ne a wani yunƙuri na tabbatar da zaman lafiya, da ɗai-ɗaito da kuma bin doka a tsakanin Mawaƙa, a ɓangaren Nishaɗi da na Addini.
“Wannan mataki ya biyo bayan wata muhawara da aka gudanar ba tare da neman izinin Hukumar ba, a tsakanin a Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi, wacce hukumar ta bayyana ta a matsayin karya dokokin aikinta”.
A yayin da yake ƙaddamar da kwamitin bincike wanda Mal. Isha Abdullahi, daraktan ayyuka na musamman na hukumar zai jagoranta, Abba El-Mustapha ya bayar da wa’adin sa’o’i 24 ga mawakan da waɗanda su ka jagoranci muhawarar tasu, da su bayyana a gaban kwamitin domin amsa tambayoyi.
“Shirya irin waɗannan muhawarori ba tare da sahalewar hukumar mu ba, ya keta dokar da ta kafa Hukumar, kuma ka iya jawo hukunci mai tsanani ga waɗanda suka aikata hakan, in ji Al-mustapha”.
Ya kuma jaddada ƙudurin hukumar na ci gaba da kula da ayyukan mawaƙa da masu nishaɗantarwa a faɗin jihar bisa doka da ƙa’ida, inda ya kuma buƙaci al’umma da su zauna lafiya, tare da bayar da haɗin kai da kawo bayanai masu amfani domin tabbatar da zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaban al’adu a jihar Kano.

