
Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke bikin paradin ranar ’yancin kai da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yanci a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025.
Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ta hannun Darektan Bayanai da Hulɗa da Jama’a, Segun Imohiosen, a cikin wata takardar da aka fitar ranar Litinin.
Sai dai Imohiosen bai bayyana dalilin da ya sa aka soke bikin ba, amma ya ce hakan ba zai rage muhimmancin wannan muhimmiyar rana ba.
A cikin sanarwar an ce:
> “Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin paradin ranar ’yancin kai da aka tsara domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 a ranar Laraba, 1 ga Oktoba.
Wannan soke bikin ba zai rage darajar wannan babban lokaci ba, domin gwamnati ta kasance a shirye wajen gudanar da sauran shirye-shiryen bikin cikar Najeriya shekaru 65 da ’yanci cikin martaba da karsashi.
Duk sauran shirye-shiryen da aka tsara domin murnar zagayowar wannan rana za su ci gaba kamar yadda aka tsara.”
Sanarwar ta kuma ce gwamnatin tarayya na ba da hakuri kan duk wata matsala ko rashin jin daɗi da wannan mataki zai iya jawo wa, tare da kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da marawa wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, baya wajen aiwatar da sauye-sauyen da za su ɗaukaka ƙasar.
> “Gwamnatin Tarayya na yaba wa fahimta, goyon baya da haɗin kan ’yan Najeriya baki ɗaya, jakadun ƙasashen waje, da kuma baki na musamman. An kuma yi kira ga ’yan ƙasa da su rungumi tsare-tsaren sauye-sauyen Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin gina Najeriya mafi girma.”
Bikin zagayowar ranar ’yancin kai na bana ya zo da taken: “Najeriya @ 65: Haɗin Kai Domin Gina Ƙasa Mai Girma

