
A karkashin wannan sabon tsari, marasa lafiya za su rika biyan Naira 12,000 kacal a kowanne wankin koda maimakon tsohon kudin da ya kai Naira 50,000.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai, Alaba Balogun, Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Tinubu na rage radadin kudi da kuma bunkasa damar samun kulawar lafiya ga ‘yan kasa, musamman masu rauni.
An fara aiwatar da shirin a asibitoci 11 na tarayya da ke cikin manyan yankunan siyasa na kasar nan, wadanda suka hada da:
Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos
Babban Asibitin Kasa, Abuja
Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Ebute Metta
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin
Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Yenagoa
Asibitin Koyarwa na Tarayya, Owerri
Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Abakaliki
Haka kuma Ma’aikatar ta karyata rahotannin da ke cewa an ware yankin Arewa maso Yamma daga shirin, inda ta jaddada cewa dukkan yankuna sun samu shiga.
“Gwamnatin Tarayya ba ta ware jihohin Arewa maso Yamma daga tallafin jinyar koda ba, sabanin yadda wasu rahotanni suka yi ikirari,” in ji Alaba Balogun, Mataimakin Darakta kuma Shugaban Sashen yaɗa labarai da Hulda da Jama’a na ma’aikatar.
Ya kara da cewa za a ci gaba da fadada shirin zuwa wasu asibitoci na tarayya domin kara yawan jama’a da za su iya amfana.
𝙶𝚊 𝚠𝚊𝚍𝚊𝚗𝚍𝚊 𝚜𝚞𝚔𝚎 𝚍𝚊 𝚋𝚞𝚔𝚊𝚝𝚊𝚛 𝚜𝚞 𝚋𝚊𝚖𝚞 𝚝𝚊𝚕𝚕𝚊 𝚔𝚘 𝚠𝚊𝚜𝚞 𝚜𝚑𝚊𝚠𝚊𝚛𝚠𝚊𝚛𝚒 𝚜𝚊𝚒 𝚊 𝚝𝚞𝚛𝚊 𝚖𝚊𝚗𝚊 𝚍𝚊 𝚜𝚊𝚔𝚘 𝚝𝚊 𝚆𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 𝚊 𝚠𝚊𝚗𝚗𝚊𝚗 𝙻𝚊𝚖𝚋𝚊𝚛 𝟶𝟿𝟶𝟿𝟿𝟸𝟸𝟸𝟸𝟷𝟷
𝚊𝚋𝚔𝚗𝚊𝚒𝚜𝚊𝟷𝟶𝟶@𝚢𝚊𝚑𝚘𝚘.𝚌𝚘𝚖


1 Comment
Jigawa