
Daga: Ahmad Muhammad Sani Gwarzo, Anipr:
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurinta na baiwa bangaren ilimi fifiko na musamman, a matsayin ginshiƙin ci gaban al’umma da makomar ƙarni na gaba, domin tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga matasa da ɗalibai a fadin jihar kano.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Makarantun Masu Zaman Kansu ta Kasa ( Private and voluntary Institutions Board), Comrade Baba Abubakar Umar Abubakar, yayin da yake zantawa da manema labarai a bikin bude gasar kwallon kafa ta cin Kofin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tsakanin kungiyar Kwallon Kafa ta Hukumar Bincike da Cigaban Ilimi ta Kano (Kano Educational Research and Development) da kuma Hadakar Hukumar Kula da Makarantun Masu Zaman Kansu, wanda Suka hadu da kungiyar mamallakan makarantu Masu Zaman kansu na Kasa reshen jihar kano Wanda aka gudanar a filin wasan makarantar sakandaren Mai Zaman Kanta ta Yan Dutse Private Senior Secondary School. Kano.
Comrade Baba Abubakar Umar ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanya ilimi a matsayin ginshikin shirinta na ci gaba, saboda tana kallon ilimi a matsayin hanya mafi dacewa da za ta kawo ci gaba, zaman lafiya, da cigaban tattalin arziki a jihar kano.
Ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Yusuf tana aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka shafi inganta makarantu na gwamnati da na masu zaman kansu, tare da samar da kayan aiki, gina sababbin ajujuwa, da kuma ƙarfafa shirye-shiryen matasa don karuwar basira da ɗa’a a cikin ɗalibai.
Da yake karin haske, Comrade Baba Abubakar Umar ya bayyana cewa gasar kwallon kafa da aka ƙaddamar tana daga cikin shirye-shiryen gwamnati na haɗa ilimi da wasanni, domin bai wa ɗalibai damar bayyana basirarsu ta jiki da ta hankali a lokaci guda, tare da gina ƙauna, haɗin kai, da ladabi a tsakanin su.
A cewar sa, “Ilimi bai kamata ya tsaya a kan karatu da rubuce-rubuce kawai ba; dole ne ya shirya ɗalibi don rayuwa baki ɗaya. Ta hanyar irin waɗannan wasanni, muna gina shugabanci, kwarin gwiwa, da hadin kai tsakanin matasan mu waɗanda su ne gobe ta Kano State.”
Ya yaba wa ƙoƙarin malamai, shugabannin makarantu da iyaye bisa sadaukarwar da suke yi wajen tallafa wa gwamnati domin ci gaban ilimi, yana mai kira da a ci gaba da haɗa kai domin cimma nasarar da ake buri.
Comrade Baba Abubakar Umar ya kuma yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki – ciki har da iyaye, shugaban nin al’umma, da masu zuba jari – da su ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen aiwatar da shirye-shiryen inganta ilimi a jihar, yana mai jaddada cewa ci gaban ilimi al’amari ne da ya shafi kowa da kowa.
Bikin ya samu halartar malaman makarantu, shugabannin ilimi, da matasa daga sassan jihar, wadanda suka yaba da irin jajircewar gwamnati wajen haɗa ilimi da wasanni domin ciyar da matasa gaba.
Sakataren Zartarwar ya ƙara jinjinawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda gwamnatinsa ke bai wa matasa da ɗalibai dama ta musamman don gina ƙwarewa, ladabi, da kishin kasa, yana mai tabbatar da cewa irin wannan gasa za ta ci gaba da zama hanya ta ƙara gina jiki da tunani ga matasan Kano domin ci gaban gaba ɗaya na jihar Kano.

