
Gwamnan Kano ya kafa kwamitin yaƙi da shaye-shaye, ya naɗa Muhuyi Magaji shugaba
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa wani kwamitin musamman domin yaƙi da matsalar shan miyagun ƙwayoyi da safararsu a jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Alhamis, ya ce an naɗa tsohon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, a matsayin shugaban kwamitin.
Sanarwar ta ce kwamitin ya haɗa da wakilan hukumomin tsaro da na gwamnati daban-daban, ciki har da NDLEA, DSS, ’yan sanda, NSCDC, Kwastam, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Hisbah da Majalisar Masarautar Kano.
A cewar gwamnatin jihar, an kafa kwamitin ne domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi wajen dakile safarar miyagun ƙwayoyi, gano masu hannu a harkar da kuma hanzarta gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa kwamitin zai jagoranci shirye-shiryen wayar da kan jama’a, musamman matasa da ɗalibai, kan illolin shan miyagun ƙwayoyi, tare da haɗa kai da cibiyoyin addini da na gargajiya wajen magance matsalar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana shan miyagun ƙwayoyi a matsayin babbar barazana ga makomar matasan jihar, yana mai cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen yaƙi da matsalar.
Ya kuma buƙaci mambobin kwamitin su gudanar da ayyukansu cikin ƙwazo da kishin jihar Kano.
Ana sa ran kwamitin zai fara aiki nan ba da jimawa ba domin jagorantar yaƙi da shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.
Ga Jerin sunayen yan kwamitin
1. Hon. A.A. Zaura – Member
2. Commander of Narcotics, NDLEA – Member
3. Coordinator, Kiru Reformative Centre – Member
4. Representative, Pharmaceutical Society of Nigeria – Member
5. Representative, Ministry of Health – Member
6. Representative, Department of State Services (DSS) – Member
7. Representative, Nigeria Police Force, Kano State Command – Member
8. Representative, Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) – Member
9. Representative, Nigeria Customs Service – Member
10. Representative, Nigeria Immigration Service – Member
11. Representative, Kano State Hisbah Board – Member
12. Representative, Kano Emirate Council – Member
13. Representative, Council of Ulama – Member
14. Maryam Muhammad, Northwest University, – Member
15. Hon. Sani Isa Romi, Senior Special Assistant Pharmaceuticals – Member
16. Amb. Yunusa Yusuf Hamza- Member
17. DCI Abba Badamasi, (Rtd.) – Member
18. Ambassador Maryam Hassan, LESPADA– Member
19. Dr. Ibrahim Garba Muhammad, Executive Secretary, Consumer Protection Council – Secretary
20. Aliyu Muhammad Sani,
Director Research and Evaluation, REPA – Co-Secretary

