
Sai dai, fadar ta jaddada cewa al’ummar Najeriya ne kawai za su yi masa hukunci a kan rawar da ya taka a lokacin mulkinsa, wanda ta ce ba za su manta da “munin mulkin Jonathan” ba.
Fadar ta kuma yi ikirarin cewa mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya sha bamban da na baya, inda ta bayyana shi a matsayin “lokacin gagarumin ci gaban tattalin arziƙi da sauye-sauyen da ke ceto ƙasar daga durkushewa.”
A cewar fadar shugaban ƙasa, masu yada batun tsayawa takarar Jonathan a yanzu suna da niyyar tayar da yaƙin neman zaɓe da wuri, abin da ta ce manufarsa ita ce rage martabar gwamnati mai ci.
Wannan martanin ya zo ne a rana guda da jam’iyyar PDP ta sanar da cewa ba za ta bai wa Jonathan tikitin tsayawa takara kai tsaye ba, sai dai ta ce yana daga cikin “zaɓuɓɓukan da take dubawa” a shirye-shiryenta na zaɓen 2027.

