
Umarnin na shugaban ƙasa ya fito ne daga zama na musamman da ya gudanar da yammacin lahdin nan a Abuja tare da Shugabannin Rundunonin tsaron kasar nan.
A cewar umarnin shugaban ƙasa, daga yanzu dukkan manyan mutane da ke buƙatar kariya za su riƙa neman jami’an tsaro daga rundinar tsaro ta Civil Defence.

