
Gwamnatin taraiya ta ci alwashin gaggauta kuɓutar da ɗaliban makarantar da ƴanbindiga su ka sace a Kebbi
Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin ceto dalibai mata na Kebbi da aka yi garkuwa da su tare da ci gaba da aiwatar da nauyin kare rayuka da dukiyoyi a ƙasar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris, ya fitar a yau Litinin a Abuja.
A cewar sanarwar, Tinubu ya jaddada cewa kare kowane ɗan Najeriya, musamman ɗalibai, nauyi ne na musamman da ya rataya a wuyan ƙasa.
Ya la’anci wannan mummunan hari da aka kai kan ɗalibai da ba su ji ba, ba su gani ba da kuma kisan malaman makaranta waɗanda suke aiwatar da muhimmin aikinsu.
Shugaban ƙasar ya kuma nuna damuwa da ta’aziyayya ga iyayen daliban mata da aka yi garkuwa da su daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati, Maga, a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi.

