
FAAC ta raba mafi girman kudin shiga a tarihin Najeriya: Naira Tiriliyan 2.225 a watan Agusta 2025.
Kwamitin Raba Kudaden Shigar Tarayya (FAAC) ya raba Naira tiriliyan 2.225 ga gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a watan Agusta 2025 wanda shine mafi girma a tarihin kasar
Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne karo na biyu a jere da aka wuce Naira tiriliyan 2 a rabon kudaden FAAC, a zamanin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Kudin sun karu ne sakamakon harajin mai da gas da VAT da kuma kudaden CET.
Daga cikin rabon Gwamnatin Tarayya ta samu N684.4bn daga kudaden haraji, jihohi kuma sun sami N347.1bn, yayin da Kananan hukumomi kuma suka samu N267.6bn, su kuwa jihohin da ke samar da mai suka karɓi N179.3bn a matsayin kason 13%.
Daga VAT N672.9bn, Tarayya ta samu N100.9bn, jihohi N336.4bn, Kananan hukumomi N235.5bn.
Haka kuma, an raba kudaden EMTL da bambancin musayar kudin kasashen waje.
FAAC ta ce jimillar kudaden shiga na watan ya kai N3.635trn, inda aka cire wasu kuɗaɗe na ayyuka, ajiya da tallafi kafin rabawa.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

