
Gwamnatin Tarayya ta ce tana shirin fadada shirin National Home-Grown School Feeding Programme (NHGSFP), domin ciyar da dalibai miliyan 50 a makarantun firamare a shekarar 2026.
Shugabar shirye-shiryen jinƙai ta ƙasa (National Social Investment Programme Agency – NSIPA), Dr Aderemi Adebowale, ce ta bayyana hakan a tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.
Ta ce shirin zai haɗa da dalibai daga aji ɗaya zuwa aji shida, har ma da yara marasa zuwa makaranta da ake shirin shigarwa a hankali.
“Ina da burin ganin cewa daga nan zuwa shekarar 2026, za mu iya ciyar da dalibai kusan miliyan 50 a duk faɗin Najeriya.”
“Za mu tattauna da manoma da masu samar da kayan abinci kan farashin da ya dace, sannan mu tabbatar da biyan kuɗi da kuma yadda ake gudanar da shirin,” in ji ta.
A ranar 27 ga watan Mayu, 2025, gwamnati ta ƙaddamar da sabon shirin Alternate Education and Renewed Hope National Home-Grown School Feeding Project a Abuja, domin ciyar da yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta da waɗanda ke cikin mawuyacin hali zuwa 2026.
Wannan shirin ya kasance wani muhimmin ɓangare na shirye-shiryen jinƙai na ƙasa (NSIPA), wanda aka ƙaddamar domin tunawa da cikar shekara biyu da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan mulki.

