
Wani mazaunin garin da bai so a ambaci sunansa cewa an kamo mutanen da ake zargi sun Kashe Dan acaban ne bayan da suka sassara shi gami da yin awun gaba da babur Dinsa kirar Bajaj ta hanyar bibiyar wayar wanda aka kashe.
“Su wannan mutane ana zarginsu da tare wani Umar Idris Dan kauyen Kamfa a karamar hukumar ta Garko, suka kwace masa Babur kafin kazo tashar ilalu bayan ya dawo daga garin Buda, suka kuma kashe shi ranar larabar da ta gabata, to bayan an bibiyi wayarsa aka kama mutane biyu da ake zargi ciki harda Dan uwan Marigayin, Bayan an kama su ne abokan sana’ar Marigayin Umar da sauran al’umma suka dage dole sai an fito musu da wadanda ake zargi suma su kashe su, lamarin da ya janyo fito-na-fito tsakanin ‘yan sanda da Al’ummar Gari,” inji Majiyar.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

