Daga Ibrahim aminu makama

A yau an gudanar da zaman sulhu tsakanin al’ummomin unguwannin Zango da Kofar Mata a Kano, domin kawo karshen rikicin da ya dabaibaye matasan yankunan biyu.
Taron sulhun, wanda aka gudanar a rufaffen dakin taro na Masallacin Shehu Ahmadu Tijjani da ke Kofar Mata, ya samu jagorancin tsohon babban jami’in soja, Mejo Janar Ibrahim Sani Yakasai (rtd.), wanda ya shiga tsakani domin tabbatar da zaman lafiya.
Janar Yakasai ya yi kira ga matasan unguwannin biyu da su rungumi hakuri da juna, yana mai jaddada cewa Zango da Kofar Mata “tamkar uwa daya uba daya ne”, don haka babu dalilin gaba.
A cikin zaman, wasu daga cikin matasan da ke cikin rikicin sun samu tallafi na sana’a a kasuwar Singa karkashin jagorancin shugaban kasuwar.
Hakazalika, masu unguwannin biyu na Zango da Kofar Mata sun yi kira ga matasan su rungumi sana’a su guji zaman banza da haddasa fitina.
Wakilinmu Ibrahim aminu makama ya ruwaito cewar taron ya samu halartar jami’an tsaro, ciki har da Baturen ‘Yan Sanda na Kofar Wambai, da masu unguwanni, da kuma dimbin jama’ar yankunan biyu, tare da matasan da rikicin ya shafa.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 09099222211 ko abknaisa100@yahoo.com

