
Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaban kasa da ci gaban al’umma.
Ministar Babban Birnin Tarayya, Dakta Mariya Mahmoud Bunkure, ita ce ta bayyana hakan a lokacin da take kaddamar da aikin bude sabon Hukumar samar da ruwan sha a babban birnin tarayya.
Ministan tace gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan ci gaban al’umma.

