
Yanzu-Yanzu: Takarar Sanatan Kano ta Tsakiya 6 Sun Janyewa Shekarau
Rahotannin da ke iske jaridar Kadaura24 na nuna cewa ‘yan takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya guda shida sun janye takararsu tare da bayyana goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, bayan wani zama na musamman da aka gudanar a yau Lahadi.
An gudanar da zaman ne karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, inda manyan jagororin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki daga Kano ta Tsakiya suka halarta domin lalubo hanyar sasanta rikicin da ya dade yana dabaibaye da takarar kujerar.
Tun bayan bayyana malam Shekarau a matsayin mai neman tikitin Sanatan Kano ta Tsakiya, an shafe makonni ana dambarwa da jan hankali tsakanin magoya bayan ‘yan takarar daban-daban, lamarin da ya haddasa rabuwar kai da zazzafar muhawara a cikin jam’iyyar APC a Kano.
Majiyoyi daga cikin taron sun bayyana cewa matsin lamba daga manyan shugabannin jam’iyyar APC a matakin kasa ne ya sanya aka gudanar da zaman sulhun, domin kauce wa rikicin cikin gida da ka iya kawo barazana ga karfin jam’iyyar a zaben 2027.
A yayin zaman, ‘yan takarar shida sun amince su janye takararsu domin bai wa Sanata Ibrahim Shekarau damar zama dan takarar da zai jagoranci tafiyar APC a Kano ta Tsakiya.
Malam Ibrahim Shekarau dai ya koma jam’iyyar APC ne a watan da ya gabata bayan shafe lokaci a jam’iyyar PDP . Sai dai duk da bai dade da shigowarsa APC ba, rahotanni sun nuna cewa shugaban kasa tare da wasu manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ne suka bukaci ya fito takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, ganin irin kwarewa da tasirin siyasar da yake da shi a Kano da ma Arewa baki daya.
Daga cikin wadanda suka janye wa malam Shekarau takarar akwai Usman Bala, Abbas Sani Abbas, Sha’aban Sharada, Dr. Muhammad Zango Fatah, Shehu Isa Driver da kuma Dr. Danyaro Yakasai.
Dama dai tun a makon da ya gabata Malam Garba Yusuf Abubakar ya fice daga cikin yan takarar tare goyawa malam Shekarau baya.
Sai dai ba a ga AA Zaura cikin wadanda suka janye wa malam Shekarau takarar Sanatan Kano ta tsakiya ba.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin matakin da aka dauka zai iya rage rikicin cikin gida da ya dabaibaye APC a Kano ta Tsakiya, tare da hada kan magoya bayan jam’iyyar gabanin babban zaben shekarar 2027.

