
Zamu bi umarnin Gwamna domin tattanawa da shugabancin Jam’iyar APC – Masu mukamin Gwamnatin Kano na Gaya.
Kamar yadda Gwqmnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin cewa duk dan Jam’iyar NNPP da yabiyoshi cikin Jam’iyar APC su hadu domin gudanar ta taron masu ruwa da tsaki na APC a kananan Hukumomi abun ba haka yake ba a karamar Hukumar Gaya.
A wani taro da suka gudanar masu rike da mukaman Gwamnati a Karamar Hukumar Gaya sun bayyana cewar tun bayan da Gwamna ya bada wancan umarni har zuwa yanzu babu wani dan tsohuwar APC da ya nemesu donin gudanar da irin wancan taro.
Akibu Sunusi Mahmoud wanda Babban Mai Taimakawa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci taron wadanda suke da mukaman Gwamnati kuma ‘yan asalin Karamar Hukumar Gaya yace su zasu shirya tareda neman ‘Yan tsohuwar Jam’iyar APC na Karamar Hukumar ta Gaya domin gudanar da irin wancan taro da tuni wasu Kananan Hukumomin suka gudanar dashi a yankunansu.
Akibu Sunusi yace tuni sunyi wani Kwaryakwaryar zama da dukkanin masu rike da mukaman Gwamnati kuma sun tattauna dukkan abubuwan da ya kamata domin tuntubar yan tsohuwar Apc na Karamar Hukumar Gaya don gudanar da taron masu ruwa da tsakin na Gaya.
Yace haduwar tasu zata kara kulla alaka da zumunci a tsakaninsu tareda mika kansu ga shuwagabanni da jagororin Jam’iyar Amana domin tafiya tare don samun nasarar jam’iyar APC a zabukan dake tafe.
Akibu yayi bayanin cewar taron zai kunshi dukkannin mazabu goma dake Karamar Hukumar Gaya na Apc da kuma ‘yan Abba Gida Gida domin kasancewa tare a matsayin tsintsiya daya.

