Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa gobara ta lalata rumfuna 529 daga cikin rumfuna na wucin gadi a Kasuwar Shuwaki da ke ƙaramar hukumar Gari, Jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Kano.
A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe 3:25 na rana daga Abdulmalik Muhammad na ofishin kashe gobara na Gari, yana sanar da aukuwar gobara a kasuwar.
Ya bayyana cewa, da zarar sun samu bayanin, hukumar ta aika jami’ai da motocin kashe gobara zuwa wurin domin kashe wutar tare da hana ta yaduwa zuwa sauran sassan kasuwar.
Saminu ya ce yankin kasuwar yana da fadin kimanin kafa 3,000 da 2,500, kuma yana ɗauke da kusan rumfuna 1,000 na wucin gadi, inda rumfuna 529 suka ƙone ƙurmus.
Sai dai ya tabbatar cewa ba a rasa rai ba a wannan hatsari.
Ya danganta musabbabin gobarar da aikace-aikacen wasu mutane masu shaye-shaye da ke zaune a cikin kasuwar.
Mai magana da yawun hukumar ya shawarci jama’a da ’yan kasuwa da su kasance masu hankali da taka-tsantsan wajen amfani da wuta da abubuwan da ke iya kama da wuta, domin kauce wa irin wannan ibtila’i a nan gaba.

