
Bambaďawa da Munafukai: Manyan Makiyan Shugabanni da Shugabanci.
A yau muna rayuwa a wani zamani da gulma, bambadanci da munafunci suka yi katutu a siyasa da rayuwar mu baki daya. Wasu Mutane da dama suna bin shugabanni ba don gaskiya da kokarin kawo cigaba ba, sai don son zuciya da neman biyan bukatar su. Wannan dabi’a barazana ce mai girma wadda ke lalata shugabanci nagari da kuma binne nagartattun manufofi.
Ina kira ga matasa: mu yi watsi da Bambaďanci, mu guji munafunci. Mu tsaya kan kyawawan manufofi da akidun da za su amfanar damu da al’ummar mu.
Mu tuna, Allah ne kaɗai mai bayar da arziƙi da rayuwa. Ɗaukar zancen wane da wane ka kaiwa wani shugaba ko mai mulki da abin duniya ba zai saka ka samu abinda Allah bai rubuta maka a kaddarar rayuwar ka ba.
Ga shugabanni kuwa, ina roƙon: ku faɗaɗa tunaninku, ku lura da bambaďawa masu munafunci da masu hada fitintuna marasa dalili. Irin wadannan mutanen su ne mafi hadari a kusa da shugaba, domin suna iya lalata tafiyar da aka dade ana shirya ta. Sau da yawa shugabanni ba sa gane illar da wadannan magulmatan suka jawo musu sai bayan lokaci ya kure kuma ba za’a iya gyarawa ba.
Saboda haka yakamata Shugabanni, ku zagaye kanku da mutane masu budadden tunani, hikima da amana waɗanda za su gaya muku gaskiya komai zafin ta.
Matasa, mu gina siyasa da rayuwa bisa gaskiya, amana da tsarkakkiyar zuciya. Wannan ita ce hanyar da za ta ci damu gaba a matsayin al’umma.
#MatasaMadogara
Taba ka lashe daga littafin: Matasa Madogara: Youth, Power and Leadership Balance.

