
Ɗan takarar mataimakin gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Murtala Sule Garo, ya shiga sahun masu taya murna a fadin Najeriya na cikar Engr. Abubakar Kabir Bichi, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bichi kuma shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, murnar cika Shekaru 44 masu albarka.
A cikin saƙon taya murna da ya fitar a ranar Laraba, Murtala Sule Garo ya bayyana Bichi a matsayin shugaba nagari kuma ƙwararren ɗan siyasa.
Garo ya ce Bichi ya nuna abin da matasa za su iya yi a shugabanci idan aka ba su dama.
Ya ƙara da cewa, jajircewarsa wajen gina ƙasa da kuma gina dan Adam abin a yaba ne, inda ya bayyana shi a matsayin matashi mai hangen nesa.
“Cikin farin ciki nake miƙa sakon taya murna a wannan rana ta musamman da kake cika shekaru 44 cikin jajircewa da ƙoƙarinka na hidima ga jihar mu ta Kano da ƙasarmu Najeriya.
“Hakika honorable Bichi ya zama abin koyi abin koyi a wurin matasa da yan siyasa.
“Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya cigaba da yi maka jagora.
“Barka da cika shekaru 44 da haihuwa tare da fatan samun ƙarin shekaru masu albarka a nan gaba.”
Murtala Sule Garo

