
ANYI KIRA NA MUSAMMAM GA AMBASSADA DACTA HALIMA SULEIMAN ZAKARI DATA FITO TA TSAYA TAKARAR SANATA A JIGAWA TA TSAKIYA A SHEKARAR 2027.
Wannan kiran ya fito ne daga al’ummar mutanen yankin kana nan hukumomi daban daban na Jigawa ta tsakiya na bukatar jajirtacciyar ‘yar gwagwarmaya Ambassada Dakta Halima Suleiman Zakari kamar yacce suka bayyana a tattaunawa da manema labarai jimkadan a wani gangami da matasan sukayi a makon da ya gabata a cewar matasaan yankin Takarar ta Ambassada Dakta Sanata Halima Suleiman Zakari ita tafi dacewa da zabin Al’ummar yankin a kakar zabe mekamawa 2027 duba da irin dinbin alheran da sukega zata fidda Jigawa ta tsakiya kunya a 2027. Kamar yacce Umar Yusuf Mahmud da Mal. Isa Dauda da Hajara Garba suka bayyana cewa muna kira da Babbar Murya gare ki da ki yi la’akari da tsayawa takarar kujerar Sanata mai wakiltar yankinmu, Bisa Ayyukan ki na Alheri da jajircewarki wajen kyautata rayuwar Al’ummarmu mun aminta da salonki bisa kowa fatan sa yana yaba miki bisa Irin namijin kokarin da kike dashi da kyawawan manufofinki a bayyane ga al’umma Jigawa ta tsakiya.
Jamaa daban daban sunci gaba da tofa Albarkacin bakinsu ganin cewa Ambassada Dakta Sanata Halima Suleiman Zakari ce amsa bisa ci gaba ta hidimtawa Al’ummar yankin da Sadaukarwarta, tausayi, da kwarewar da take da ita wajen jagoranci wanda a fili yake ta dacewa da wannan mukami na Sanatan Jigawa ta tsakiya a 2027 insha Allah. Mun yi imanin cewa wakilcin nata zai kawo sauyi mai kyau da inganci da cigaba da wadatarda dinbin Jama’ar yankinmu tabbas zamuyi da fifi ganin kin dore wannan kujera ta Sanata domin cigaba da kawonana Abubuwan more Rayuwa a Jigawa ta tsakiya.
Ambassada Dakta Sanata Halima Suleiman Zakari muna rokonki da ki fito ki amsa kiraye kirayenmu domin amsa wannan takara ta Sanata ki tsaya takarar nan don Bunkasa Rayuwar Al’umma, haka kuma muna kira ki yi amfani da karfinki wajen kara wa muryar Al’ummarmu Amo. Jajircewarki wajen inganta rayuwar al’umma Jigawa ta tsakiya tabbas zai bar tarihi mai dorewa da Nasara a yankin mu na Jihar Jigawa abun alfaharun mu.
Wannan Sako ne daga Dandazon Masoya, Magoya bayan Ambasada Dacta Sanata Halima Suleiman Zakari 2027.

