
A madadin Shugabar Matan Jam’iyyar APC ta Jihar Kano, tana mik’a sak’on taya murna ga Rt. Hon. Abubakar Kabir Bichi, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Bichi, a wannan rana ta zagayowar ranar haihuwarsa.
Hon Abba Bichi, ya kasance abin koyi ga ‘yan siyasar Nijeriya baki ɗaya, yana gudanar da jagoranci na gaskiya, tawali’u da kuma jajircewa wajen yiwa al’umma hidima. Kokarinsa da nasarorin da yake samu suna cigaba da zama abin koyi ga matasa da manya a ciki da wajen yankin sa na Bichi.
Yayin da muke murnar wannan rana ta musamman, muna yi maka fatan alheri tare da samun ƙoshin lafiya, hikima, da ƙarin nasara wajen yiwa ƙasarmu hidima. Allah ya kawo maka farin ciki, cikar buri, da nasarori masu yawa a wannan sabuwar shekara ta rayuwarka.
Barka da Zagayowar Ranar Haihuwa, Rt. Hon. Abubakar Kabir Bichi! 🎉🎂
Sak’o daga:
Hajiya Fatima Abdullahi Dala.
Shugabar Matan APC, Jihar kano

