
Jam’iyyar APC a ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji tayi babban kamu na komawar dumbin ‘yayan jam’iyyar PDP masu biyayya ga Hon. Dr. Adamu Dan Gwani tsohon kwamishina kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano.
Taron karɓar ‘yayan jam’iyyar PDP wadanda Dr. Dan Gwani ya jagoranta yau a garin Kafin Maiyaki ya samu halartar shugabanni da jagororin jam’iyyar APC na Kiru da Bebeji Hon. Sanusi Kiru Majidadi Hon. Kabiru Hassan Dashi, Jagora Alh. Abubakar Me Mai tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Kiru da Bebeji Hon. Muntari Isyaku Kmaiyaki Hon. Mudan Umar Bebeji Hon. Ahmad Rufa’i Garba Yalwa, tsofaffin kansilolin Kiru da Bebeji da sauran shugabannin jam’iyyar da magoya baya.
A madadin shugabancin jam’iyyar APC na Kiru da Bebeji muna musu barka da shigowa gidan ‘yanci da siyasa mai tsafta. Allah Ya karawa jam’iyyar APC farin jini da nasara Ameen.

