
Injiniyya Abba Ganduje Ya Amince da Bawa Wadannan Rukuni Kayayyakin Dogaro da kai Tare da Umarnin Raba Kayan a Yau Talata a Dawakin Tofa Rimingado da Tofa .
Babban Direktan Fasaha na Hukumar samar da Wutar Lantarki ta kasa (REA ) Engr Umar Abdullahi Ganduje FNSE Ya Amince da Bawa Wadannan Rukuni Kayayyakin Dogaro da kai a Kananan Hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa Rukunin sune kamar Haka..
Dattawan Jam’iyya (Coucas) na kowacce Karamar hukuma Dake Kananan Hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa, Buhunan shinkafa buhu 40 takin Zamani Buhu 50 Baburan Hawa guda 5, Tare da Injin Ban Ruwa guda 5 kowacce Karamar hukuma.
Sannan ya Bawa Tsofaffin Kansilolin mulki Injin Ban Ruwa kowanne, Haka kuma ya Bawa kowanne Adviser, supervisor, injin Ban Ruwa Kowacce Karamar hukuma.
Bugu da Kari Ya Bawa kowacce shugabar Mata matakin Karamar Hukuma (Local Government woman leader) Keken Dinki da kuma injin markade.
Engr Ganduje Ya Amince da Bawa LG Excos injin Ban Ruwa kowanne, Tare da Ward party chairman da kuma Sakatarorinsu kowanne injin Ban Ruwa.
Sai kuma Shugabar mata (Ward woman leader) suma injin markade, da kuma Wakilansa Na Mazabu wato Abba Ganduje coordinator takin zamani da injin Ban Ruwa…
Engr Ganduje ya Bawa Matasa Yan tauri kowacce LG takin zamani da baburan Hawa, Tare da Yan Social media kowacce LG shinkafa buhu 20 takin zamani buhu 50 da kuma baburan Hawa.
Ward excos Kowacce Karamar Hukuma Buhun takin zamani Tare da Ulama sun Rabauta da Takin Zamani buhu 20 kowacce Karamar Hukuma…
Daga Karshe Engr Ganduje ya Bada Umarnin Bada Kayan Yau a Wuraren da Ake Karbar Kayayyaki Makamancin Wannan a Kowacce Karamar Hukuma.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

