
Murtala Sule Garo ya taya T. Gwarzo murnar cika shekaru 65 a duniya
Ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen 2023, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya Girma tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma tsohon ministan gidaje, Engr. Abdullahi Tijjani Gwarzo murnar cika shekaru 65.
A cikin gaisuwar taya murna da ya fitar ranar Laraba, Garo ya bayyana T. Gwarzo a matsayin jagora nagari masanin siyasa, jajirtacce wanda rayuwarsa ke cike da tawali’u da kuma hidima ga al’ummar jihar Kano da Najeriya gaba daya.
Ya yaba wa T. Gwarzo bisa yadda yake tafiyar da rayuwarsa cikin hidimtawa al’umma tun daga tushe har zuwa lokacin da ya zama mataimakin gwamnan Kano da kuma lokacin da aka nada shi karamin ministan gidaje da tsara har zuwa yau.
“Ina cike da farin ciki da godiya ga Allah SWT nake a yayin mika wannan gaisuwar ta taya murna ta musamman a wannan rana da kake cika shekaru. A yau ba wai kawai muna murnar zagayowar ranar haihuwarka ba, muna taya ka murna bisa yadda kake gudanar da rayuwarka abar koyi ta hanyar hidimtawa da sadaukar da kai ga al’ummar Kano da Kasa baki daya.
“Ina godiya ƙwarai bisa shawarwari da kalmomin karfafa gwiwa da ake bamu tsawon shekaru tare da addu’ar Allah ya kara maka lafiya da karfin gwiwa domin a cigaba da hidima ga al’umma. AMEEN
Barka da cika shekaru 65 masu albarka.
Murtala Sule Garo

