
Ina ganin kamar jagororin APC a Kano basu fahimci matsalolin Da suka fuskanta ba a kakar Zaben 2019 da 2023 ta yadda zasu Yi Gyara Don fuskantar Zaben 2027 ba – Abdullahi Musa Gwale
ALLAH ya Sani Ina cike da dukkanin tuhumar Jagororin APC a Ko wanne mataki a jihar Kano
Tun bayan Zaben da ya Gudana a tsakanin Ganduje/Gawuna da Abba/ Comrade a shekarar shekarar 2019 a inda karfin Jam’iyyar ya bayyana a yankin Kano ta kudu Data Arewa Aka Samu Koma baya a Kano ta tsakiya a inda kwankwasiyya suka tsaya suka Yi gyare gyare Don Samun nasara masamman a kudancin Kano
A inda suka Samu Nasarar karbar da yawa daga cikin Zababbun mu Irin Su Rt. Hon. Kabiru Alasan
Hon. Kofa
Da Kuma tsayar Da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya
Abinda na Sani Duk lokacin da Aka Yi Zabe tilas a dawo Drowning board a Koma Ko wanne poling Unit da Aka Samu Nasara a ci gaba da Tabbatar da wannan nasara
Haka Kuma Duk inda Aka Samu Matsala a kalli sababin matsalar Don Daukar mataki da Tabbatar da
Work plan
Swort Analysis
Action plan
Visibility Studies
Domin Samun cikakkiyar nasara
Amma Sai dai Kash ba haka Ake a APC Kano
Abinda Zai tabbatar Mana da haka a Zaben 2019
An Samu cikakkiyar Matsala a mazabu Kano central Kuma Babu abinda Aka Yi Don Gyaran wannan Matsala
Dan haka Da Zaben 2023 ya dawo a haka Aka shiga da Dukkanin matsalolin ba tare da Gyaran ko wacce
A Shugabancin APC ba’a karbar shawara ba’a yin Meeting a bada damar kowa ya bada gudunmuwa a ko wanne mataki
Ana fifita magulmata da Yan Kore da Rashin yadda da cewar wane suna bada gudunmuwa
Haka ya faru bayan Zaben da Aka Yi da ya bawa Abba nasara Babu inda Aka kirawo mutane Aka basu hakuri ko Aka Yi sulhhunta Wasu da Aka San suna da Wani Sabani Tun daga Kan Yan majalissar Taraya/Jiha/ ciyamomi wacce a kanan hukumomi 44 Babu inda Babu irin wannan gillin
Bayan an Samu Gwamnatin Tarayya haka Aka cu Gaba Da baiwa Yan jam’iyyar APC mukamai a tsarin Kuma izuwa Yanzu ALLAH ne kadai yasan mukaman da suke Kano Amma shin mukaman kwalliya Tana biyan kudin sabulu ko kuwa kowa yaji Abinda Hon Murtala S. Garo ya fada a Taron Masu Ruwa da tsaki da ya Gudana a Abuja
Ina ganin ba Daidai bane jagororin Jam’iyyar a matakin Jiha Su Fara maganar wane ya kamata a tsayar Domin Samun Nasara ba
Kamata yayi Ace an mayar da Hankalin Yan jam’iyyar APC Zuwa ga Amincewa da Duk abinda jagororin Jam’iyyar suka Amince ya Zama matsayar mu ta Gaba Daya
A Gina jam’iyyar a samar da ofisoshi da Kuma shirya Duk Wasu Tarurruka a mazabu da Kuma kanan hukumomi 44
Amma Kash Sai Aka Fara da rigimar Ni wane nake so ya Samu Takara Ni wane nake so ya bawa takara
Cikin Mutuntawa nake son mu kalli mafiya yawan Masu wannan maganar basu ci amwatin Su ba Kuma basu San me yahana Su cin Zaben ba
A Don haka muke bada Shawara a Koma mazabu a tabbatar Da Masu Ruwa da tsaki wadanda suke bawa jam’iyyar APC Gudunmuwa
A zauna da Su a tabbatar Da korafe korafen suna cikin APC
Duk Wanda Zai ce Maka APC zata Yi nasara Babu Gudunmuwar Sanatan Barau ko Excellency Nasiru Yusif Gawuna ko za’a Yi nasara ba Tare da HE. Murtala S Garo Ko za’a Yi nasara Babu irin Su AA zaura da Sauran Su to gaskiya ya kamata a Kai Shi asibitin Dawanau
Haka Kuma Tilas kamar yadda Muka rinka fada Babu Dan Gata a APC kamata yayi kokarin da mutum yake na Gina jam’iyyar APC Yana cikin abinda zamu kalla wajen Bawa mutane Takara
Amma kuskure ne matuka Ace mutum Yana bada gudunmuwa matuka Amma a Koma a Ware Wani Dan Gata a rinka alkawarin takara ga Wasu a irin wannan lokaci Rauni za’a Yi wa wannan jam’iyyar APC
A karshe mu cire hassada Da Bakin ciki mu hadu Don Samun cigaban wannan
Mu hada Kai ba wai hadin baki ba
Kowa yasan Wanda ya Fi Shi ya Zama Muna da sadaukar wa
Wallahi matukar muka tafi a haka zamu Samu matsalar
Kowa ya taimaki mutane ko ka San su Ko Baka San Su ba
A cikin abinda Muka Kai Kara a Zaben da ya wakana mun ga Irin matsalolin Agent suka tafi da Nasarar APC
Shin irin Tarkacen da Muka Kai a matsayin agent irin Su zasu mu tura ko kuwa??
A Yanzu Muna Da cikakken lokaci Tilas muyi amfani Da Shi don Yin shiri Na masamman don Samun cikakkiyar nasara
Wannan Shine tunani na kuna tilas a Yabawa irin Yan majalissar mu tun daga Kan sanatocin mu da ma ragowar Rep’s da Yan majalissar jiha
Da tsofaffin ciyamomi da kansiloli
A karshe nake Kiran mutane Su dage da Addu’a da Kuma posting na hadin Kai
Ku Dena ruduwa da kusakuran Yan gwari
ALLAH ya taimaki Kanon Dabo ya tsare Mana kasuwancin mu da Malaman mu da mutuncin wannan gari

