
AN ZARGI SHUGABAR KARAMAR HUKUMAR TUDUN WADA DA NUNA BANBANCI TSAKANIN KANSILOLIN KARAMAR HUKUMAR
Kasancewar kansiloli sune ke kusa da Jama, a wadanda ana iya cewa sune ma,aunin farko na tsarin gwamnati Wanda daga kansune ake fara ganin yunkurin gwamnati na bazawa JAMA,a Ayyuka ko akasin haka.
Sai gashi kuma karamar hukumar Tudun wada ta yi bonanzar miliyoyin kudi ga wasu daga cikin kansilolin da suke Yan mowa yayinda wasu kuma ake zargin karamar hukumar ta yi kememe ga sauran kansilolin da aka zabe su da shugaban karamar hukumar.
Wannan batu ne yake tada hazo a yankin karamar hukumar Tudun wada,domin kuwa sauran kansilolin da ba,a baiwa miliyoyin kudinba suka koka,da yanzu haka ma,sun fara rubutawa kwamitin majalisar Dokokin jihar kano akan harkokin kanana hukumomi takardar korafi domin suma su sharbi romon dimukradiyya,harma yayi naso zuwa ga masu ruwa da tsaki.
Sai dai wata majiya ta bayyana cewar anware kansilolin ne bisa yadda shugabar karamar hukumar take zargin kansilolin da marawa Dantakarar jam, iyyar APC baya, wadda suma yayan jam, iyyar ta APC ne tunda Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf shima Dan jam, iyyar APC ne tun daga sama har kasa.
Idan har batun da ake bayyanawa gaskiya Babu shakka akwai tsumbure a yankin karamar hukumar Tudun wada,game da Babban zabe mai zuwa,bisa ga Dukkan alamu ana neman yiwa. Zaben shugaban kasa rauni da Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf da sauran masu neman kujeru na Apc.
Yakamata Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ya sanya Idanunsa a yankin karamar hukumar Tudun wada,dan kar azo ayi masa sakiyar da ba ruwa tunda yanzu an fara ta kan kansiloli,ba,asan wajen da abin zai tsaya ba,ko dai Gwamnan yaci zabe ko kuma akasin haka.

