Screenshot 20251219 180350

’Yan Majalisa sun ƙi amincewa da bukatar haramta sayen ƙuri’a a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyu

 

Majalisar Wakilai ta ƙi amincewa da wani kuduri da ke neman mayar da ba da kuɗi ko kayan alatu domin rinjayar masu zaɓe a lokacin fidda gwani na jam’iyyu a matsayin laifi.

 

’Yan majalisar sun kaɗa ƙuri’a na kin amincewa da kudurin ne a ranar Alhamis, yayin nazarin rahoton da ke neman gyara Dokar Zaɓe ta 2022.

 

Wani sashe a cikin rahoton ya tanadi cewa duk wanda ya ba wakili kuɗi ko wani abu na kuɗi domin karkatar da sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyya, zai fuskanci hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari ba tare da zaɓin tara ba.

 

Sashe na 89(4) na rahoton gyaran dokar ya ce: “Duk mutumin da ya ba wakili kuɗi ko kayan alatu domin rinjayar sakamakon fidda gwani, taruka (congresses) da manya tarukan (conventions) na jam’iyya, ya aikata laifi kuma idan aka same shi da laifi, za a yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari ba tare da zaɓin tara ba.”

 

Sai dai ’yan majalisar baki ɗaya sun ƙi amincewa da sashen, lokacin da shugaban zaman, Benjamin Kalu, ya nemi a kaɗa ƙuri’a ta hanyar murya.

Daily Nigeria Hausa

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version