IMG 20260430 164817 481

Majalisar Zartarwar Kano Ta Amince da Kashe Sama da Naira Biliyan 61 Don yi muhimman aiyuka

Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da kashe jimillar kuɗi har Naira biliyan 61.63 domin aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na jihar.

An cimma wannan matsaya ne a yayin zaman majalisar karo na 39 da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan ga manema labarai .

Ya ce amincewar da aka bayar na daga cikin ƙudirin gwamnatin jihar na inganta rayuwar al’umma da kuma ci gaba da aiwatar da ayyukan more rayuwa a faɗin Kano.

Ilimi Ya Samu Gagarumin Kaso

A ɓangaren ilimi, majalisar ta ware sama da Naira biliyan 4.45 domin biyan kuɗaɗen jarabawar NECO, NABTEB da NBAIS ga ɗaliban da za su rubuta jarabawa a shekarar 2026.

Haka kuma, an amince da Naira biliyan 2 domin samar da kujeru da tebura a makarantu da ke ƙananan hukumomi 30, tare da gina da gyaran azuzuwa a Makoda, Tarauni, Ajingi da Minjibir.

Majalisar ta kuma amince da biyan wasu basussukan kuɗaɗen jarabawa daga shekarar 2020 zuwa 2023, da kuma kuɗin ciyar da ɗaliban makarantu masu kwana.

Lafiya da Rigakafi

A fannin lafiya kuwa, gwamnatin ta amince da gyaran Babban Asibitin Wudil tare da samar da kayan aiki na zamani ga wasu asibitoci.

Haka kuma, an ware kuɗaɗe domin shirye-shiryen rigakafi da yaƙi da cutar shan inna a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Sannan za a samar da kula da lafiya kyauta ga mata masu juna biyu, jarirai da ƙananan yara a cibiyoyi 484.

Hanyoyi da Ababen More Rayuwa

Majalisar ta kuma amince da kashe sama da Naira biliyan 5.2 domin gina hanyar Panshekara Underpass zuwa gadar Madobi, tare da gyaran hanyoyi a ƙaramar hukumar Gwale.

Sauran ayyukan sun haɗa da gyaran ofisoshin gwamnati da inganta sansanin horas da matasa na NYSC da ke Kusalla.

Noma da Ruwan Sha

Domin bunƙasa noma, an ware kusan Naira biliyan 3.5 domin sayen takin zamani sama da buhu 41,000 tare da ƙarfafa harkokin ban ruwa.

A Karon Farko Abba Gida-gida ya bayyana dalilin zabar Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Kano

A ɓangaren ruwa kuwa, gwamnatin ta amince da Naira biliyan 3.48 domin gyaran matatar ruwan Tamburawa da kuma samar da rijiyoyin burtsatse a wasu yankuna.

Gwamnati Ta Jaddada Gaskiya

Kwamishina Waiya ya tabbatar da cewa za a gudanar da dukkan ayyukan cikin gaskiya da bin doka, yana mai cewa gwamnatin Kano na da burin isar da ribar dimokuraɗiyya ga al’umma tare da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version