1778168134567

Gaisuwar da na yi wa Sanusi a taro ba ta na nufin mubaya’a nai masa a matsayin shi ne Sarkin Kano ba – Ganduje

 

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce kotun koli ce za ta yanke hukunci kan rikicin masarautar Kano.

 

Ganduje, wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC ne na ƙasa, ya bayyana cewa gaisuwar da ya yi wa Muhammadu Sanusi II a wani taron gwamnati kada a ɗauke ta a matsayin ya masa mubaya’a a matsayin Sarkin Kano.

 

TheCable ta rawaito cewa a lokacin rantsar da sabon mataimakin gwamnan Kano ranar Talata, Ganduje ya kira Sanusi da “Sarkin Kano kuma shugaban majalisar sarakunan Kano”, lamarin da ya jawo tafi daga mahalarta taron.

 

A cikin wata sanarwa da Muhammad Garba, tsohon shugaban ma’aikatan Ganduje, ya fitar, tsohon gwamnan ya ce kiran Sanusi da Sarkin Kano a wajen taron “girmamawa ce kawai da aka saba yi a irin taron jama’a”.

 

Ganduje ya ƙara da cewa kotun koli ce za ta yanke hukunci na karshe kan rikicin sarautar, yana mai cewa ba shi da ikon doka na “amincewa ko kin amincewa da duk wani mai neman sarautar Kano”.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version