
Da yake jawabi lokacin taron Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero yace ana shirya wannan taron ne duk shekara a irin wannan rana ta farkon watan Zul hijja.
Yace za’a gabatar da Karatun Qur’ani tareda yin sauka har dubu Goma a cikin kwanaki Goma, duk domin neman yardar Allah tareda neman kriyarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace haka Kuma anayin adduo’in neman zaman lafiya ga Kasa da jihar Kano tareda neman karuwar arziki da Kuma kwanciyar hankali.
A lokacin taron Liman Malam Muhammadu Kamalu yayi adduo’i na Musamman ga Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero kan Allah ya bashi rinjaye akan makiynsa tare bashi Nasara akan duk abunda yasa a gaba.
Zadai a cigaba da gudanar da Karatun Qur’ani Mai tsarki har zuwa ranar 10 ga wata inda za’ayi khatmar Karatun.