
Musa Iliyasu Kwankwaso ya jinjina wa Shugaba Tinubu kan hana karkatar da kudaden Kananan Hukumomi.
Jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kano Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya nuna goyon bayan sa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan dagewar sa kan lallai sai Kananan Hukumomi sun sami yancin karban kudaden su kai tsaye daga Gwamnatin Tarraya. Yace hakan biyayya ne ga doka sabanin zargin cimma burin siyasa.
Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso da a yanzu shine Babban Daraktan Kudi a Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are ya jaddada cewa baiwa Kananan Hukumomi damar cin gashin kansu ginshiki ne na samar da cigaba daga kasa kuma zai samar da daidaito a Kasa.
Kwankwaso wanda ya Shugabanci Karamar Hukumar Madobi har sau biyu lokacin mulkin Tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa umarnin Shugaba Tinubu na bawa Kananan Hukumomi kudaden su kai tsaye na nuni da sanin matsalolin dake dakile da zama tawaya ga cigaba musamman daga kasa.
Yace ” Wannan babu batun siyasa sai kokarin ceto tsarin gudanawa daga kasa”.
Kwankwaso ya bayyana cewa bawa Kananan Hukumomi ikon sarrafa kudaden su zai karfafe su wajen kawo karshen rashin aiki yi da rashin tsaro da karancin kayayyakin more rayuwa.
Musa Iliyasu Kwankwaso yayi bayanin cewa yayin da Kananan Hukumomi suka sami ikon sarrafa kudaden su zasu samar da ayyukan yi ga matasa da taimakawa kungiyoyin sa kai dan samar da tsaro da hakan zai bada damar dakile barazanar tsaro a take . Ya kara da cewa baiwa Kananan Hukumomi ikon sarrafa kudaden su kai tsaye zai dawo da cigaba ga Al’umma. Karban kudaden su kai tsaye zai bawa Kananan Hukumomi damar samar da ayyukan da Al’ummar su suka fi bukata kamar Asibitoci da makarantu da tituna da matakan tsaro sabanin dogon jira daga gwamnatin jiha.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bada misalai kan yanda ya samar da ayyukan cigaban a lokacin da yake Shugaban Karamar Hukumar Madobi. ” Lokacin da nake shugaban Karamar Hukuma kimanin shekaru 20 da suka wuce Karamar Hukumar Madobi na karban kudin akalla Naira Miliyan 30 duk wata. Bayan biyan albashi na kusan Miliyan Tara mu samar da ayyukan cigaba da har yanzu Al’umma na morar su.
Ya kwatanta da abinda ke faruwa a yanzu inda Kananan Hukumomi ke karban makudan kudade amma babu wasu kwararan ayyuka a kasa. Ya bada misali cewa a yanzu Karamar Hukumar Madobi na karban fiye da Naira Biliyan daya kowane wata amma tunda daga Jiha ake bada umarnin yanda za’ayi da kudaden da wuya a gan ayyukan cigaba a kasa.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kara da cewa batun bawa Kananan Hukumomi ikon sarrafa kudaden su ba umarnin Shugaba Tinubu bane hukuncin Kotun Koli ne. ” Gwamnoni ya kamata su girmama hukuncin Kotun Koli in har da gaske suna biyayya da girmama hukuncin Kotu.
Yayin da yake bayani kan kasafin kudi na shekarar 2016 Musa Iliyasu Kwankwaso yana da kyakyawan zato da fata inda ya lissafo wasu ayyukan cigaban kasa da aka cigaba da yin su a fadin Najeriya kamar titin Jirgin Kasa daga Kano zuwa Maradi da Kano zuwa Abuja da manyan ayyuka da ake cigaba da yin su na nuni ga dorewar cigaba.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma yaba da cigaba da ake samu a harkar tsaro inda ya jinjina wa Malam Nuhu Ribadu da manyan jagororin tsaro. ” Wurare kamar Birnin Gwari da hanyar Abuja zuwa Kaduna an sami saukin barazanar tsaro. Sannan ana ta kokarin kawo karshen rashin tsaro a Jihohin Zamfara da Sokoto.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma yi watsi da kalaman cewa Shugaba Tinubu na fuskantar adawa mai karfi a Arewa. Yace mutane suna da kyakyawan fata da zato ga Shugabancin Shugaba Tinubu. ” Daga Kano zuwa Maiduguri da Arewa ta tsakiya Shugaba Tinubu na da goyon baya”. Yan Najeriya suna ganin cigaban da ake samu karkashin mulkin Shugaba Tinubu kuma zasu saka da alheri in lokaci yayi.