1757352563202.Screenshot 20250908 182835

YA KAMATA A DAWO DA BADA KATIN ZABE A MAZABU – MALAM ABDULLAHI ZARIA

Wani magidanci dake zaune Garin Zaria yayi wannan Kiran ga Hukumar Zabe ta Kasa, a lokacin da ya wuni cir Domin karba katin Zaben a ofishin Hukumar Zaben dake yankin Karamar Hukumar ta Zaria.

Malam Abdullahi yace mafi yawa daga cikin masu karbar Katin zaben wadanda suke da kishin yin Zabe ne amma Kuma suna shan wahala wajan bin layin karbar katin Zaben bayan nisa daga inda suka bari zuwa Hukumar Zaben dake Karamar Hukumar su.

A maimakon Hakan yace ya kamata a duba Yuwuwar komawa tsarin da ake dashi a baya na komawa kowacce mazaba inda akwatin Zabe yake Domin bawa al’uma damar karbar Katin zabensu.

Ya Yabawa Hukumar Zaben ta kasa bisa yadda take kokarin bayar da Katin zaben a hedikwatar Hukumar dake kowacce Karamar Hukuma ammafa kamar yadda yace “idan har anaso al’uma su sami karbar Katin to a duba Yuwuwar komawa mazaba”.

Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version