IMG 20260723 WA0245

Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk Umar ya nada Sheikh Abdulkadir Jiyali a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa.

Sarkin na Daura Alhaji Umar Farouk yace bayan zama da “Yan Majalisar Masarautar ta da Daura sukayi sunga Cancanta da Kuma dacewar nada Sheikh Abdulkadir Jiyali a wannan Matsayi bisa wasu dalilai.

Dalilan sun hada da himmar da Shehin Malamin yake da ita wajan cusa Soyayyar Annabi Muhammadu SAW a zukatan Al’uma da Kuma ganin anyi biyayya ga Umarninsa da yin aiki da koyarwarsa.

Takardar nadin ta kara da cewa a irin wannan lokaci da ake ciki na tabarbarewar Zamani abunda Sheikh Jiyali yakeyi shine baunda ya dace domin dora Al’umar Musulmi kan Tafarki na Gaskiya.

A maimakon jama’a su kasance masu shagaltuwa da neman Duniya kawai akwai bukatar su kasance masu neman lahirarsu ta hanyar yin riko da kyawawan ayyuka irin Wadanda Shugaban Halitta Annabi Muhammadu SAW ya koyar.

Daganan takardar Wadda Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr Umar Farouk ya sanyawa hannu ya taya Sheikh Abdulkadir Jiyali Murnar wannan sarauta tareda tabbatar masa da cewa nan gaba kadan Majalisar Masarautar zata sanya ranar da za’ayi Bikin nadashi a wannan Matsayi na Sarkin Takutahar Kasar Hausa.

PR/ABK
23/07/2026

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version