
Wannan mataki ya nuna ƙaunar da gwamnati ke yi wa addinin Musulunci, malamai, da kuma al’ummar Darikar Tijjaniyya. Haka kuma, ya ƙara tabbatar da matsayin Jihar Kano a matsayin cibiyar ilimi, zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban addini.
Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa Mai Girma Gwamna da alheri, Ya ƙara masa lafiya, hikima da nasara wajen jagorantar al’ummar Jihar Kano, Ya kuma sanya wannan aiki nasa ya kasance cikin manyan ayyukan alheri da za su amfane shi a duniya da lahira.
Allah Ya ci gaba da ɗaukaka Jihar Kano, Ya tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmi da Najeriya baki ɗaya.
Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh.
Sa Hannu:
Imam Shehu Tasiu Ishaq, JP
Babban Sakatare
Daga janiin yada Labaran kungiya
Abubakar Balarabe kofar naisa