
Rikicin cikin gida ya ɓarke tsakanin ƴan ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa a Najeriya
Daga Comrade-Zakari Y Adamu Kontagora
Rahotanni na cewa rikicin ƙarfin iko tsakanin ƴan kungiyar ta’addanci ta Lakurawa ya ɓarke, kuma ya na ci gaba da ƙamari, inda jagoran yankin Arewa maso Yamma na ƙungiyar, Dando Sibu, wanda ba ɗan Najeriya ba ne, ya ke fuskantar saɓani mai tsanani da ɗaya daga cikin manyan kwamandojinsa, Kachalla Ibn Zaidu, ɗan asalin Jihar Borno.
Majiyoyi sun ce Kachalla Ibn Zaidu ne ke da alhakin yawancin hare-haren da ‘yan Lakurawa ke kaiwa a Jihar Kebbi. Yanzu ƙungiyar ta shiga irin halin da Boko Haram da ISWAP suka tsinci kansu a ciki, domin duka bangarorin biyu, Dando Sibu da Kachalla Ibn Zaidu, suna shirye-shiryen kai wa juna hari domin kashe juna.
Masu lura da harkokin tsaro ciki harda Shehu Umar, na ganin wannan rikicin a matsayin labari mai daɗi ga Najeriya saboda zai raunana ayyukan ta’addanci a yankin.