
Malamin addinin Musuluncin nan dake Kurnar Asabe a Kano Sheikh Jiyali Abdulkadir AlMunsheed kamar kowacce Shekara irin wannan ya jagoranci Dubunnan al’uma Domin Gabatar da zagayen Maudin fiyayyen al’uma shugaban kowa a duniya da lahira Annabin Tsira Annabi Muhammadu SAW.
Kamar dai yadda ya saba shehin Malamin yayi zagayen tareda al’umarsa ana Bandiri davrera Salatin Manzon Allah da Kuma wakokin yabo ga Annabi Muhammadu SAW.