
shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ya yabawa Babban Daraktan Hukumar NPC Dr. Baffa Babba Dan Agundi bisa yadda a kowanne wata yake baiwa matasa kayayyakin sana’o’i daban daban a jihar Kano. kayayyakin da ya bayanasu da cewa sunada muhimmanci kwarai da gaske wajen cigaban matasan.
“Wadannan kayayyaki irinsu Babur mai kafa uku da kuma mai kafa biyu da kudade da sauran abubuwan cigaban matasa da kake basu muna jin dadi kwarai da gaske kuma muna kira ga yan Jam’iyar mu ta APC masu mukami suyi koyi da kai Baffa Babba Dan Agundi tareda hadin kan “Yan Jam’iyyar mu ta APC a jihar Kano domin tunkarar nasara a shekara ta 2025 inji Abdullahi Abbas”.
Manoma dubu daya ne (1,000) ne dai suka Amfana da Takin noma domin amfani dashi wajan inganta nomansu