Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta Babban Birnin Tarayya (ARD-FCT) ta sanar da shiga yajin aikin gargadi na kwana bakwai, saboda matsalolin da suka ce sun addabi tsarin kiwon lafiya a Abuja.

Sanarwar ta fito ne daga shugabannin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugaban ARD-FCT, Dr. George Ebong, wanda ya bayyana cewa matsalolin da suka haddasa yajin aikin sun haɗa da:

Karancin ma’aikatan lafiya

Kayan aiki marasa inganci

Matsin lamba ga likitoci wajen gudanar da ayyuka

Rashin biyan alawus na musamman

Dr. Ebong ya ce yawancin likitoci suna tilasta gudanar da aiki a sassa da dama lokaci guda, saboda ƙarancin ma’aikata, abin da ke haifar da gajiya da kuma barazana ga ingancin kulawar lafiya da ake bai wa marasa lafiya.

A cewarsa, tun a watan da ya gabata ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki kan waɗannan matsaloli, amma har yanzu ba a ga sauyi ba.

Ƙungiyar ta yi gargadi cewa idan aka ci gaba da yin watsi da bukatunsu, hakan na iya jefa tsarin kiwon lafiya gaba ɗaya cikin mummunan rikici a Babban Birnin Tarayya.

Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version