1757855285480.Screenshot 20250914 140735

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Za A Samu Ambaliya A Wurare 32, Ciki Har Da Kano.

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wurare 32 da ke cikin jihohi 11, ciki har da Jihar Kano, daga ranar 14 zuwa 18 ga Satumba, 2025. Hasashen na zuwa ne sakamakon ruwan sama mai tsanani da ake sa ran zai ratsa sassan ƙasar nan a makon nan.

‎Sanarwar ta fito ne daga Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta hannun Cibiyar Hanyar Farko ta Kasa kan Ambaliya, wacce Darakta Usman Abdullahi Bokani ya rattaba wa hannu.

‎Jihohin da ke cikin haɗari sun haɗa da Adamawa, Benue, Nasarawa, Taraba, Delta da Neja, tare da wasu yankuna a Kebbi, Kano, Katsina, Sakkwato da Zamfara. A cewar sanarwar, karin ruwa a kogunan Gongola, Benue da Neja ya ƙara tayar da barazana, inda aka shawarci al’ummomin da ke bakin koguna da su gaggauta barin wuraren kafin lamarin ya tsananta.

‎Gwamnatin ta kuma yi kira ga Gwamnatocin jihohi da cibiyoyin bada agajin gaggawa da shugabannin al’umma da su ɗauki matakai cikin gaggawa domin rage yiwuwar asarar rayuka da dukiyoyi da ambaliyar ka iya haifarwa.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version