
Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana yadda hukumar ta samu ragin fiye da Naira biliyan 19 daga farashin aikin Hajjin shekarar 2025 domin mahajjatan Najeriya, gabanin aikin Hajjin 2026.
Farfesa Usman ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a isar Kano a yau Juma’a, bayan dawowarsa daga Saudiyya inda ya kai wata ziyarar gaggawa a ranar 22 ga Satumba don tattaunawa kan inganta ayyuka da rage farashi ga ƴan Najeriya da ke shirin zuwa Hajjin badi.
A cewarsa, an samu wannan rangwame ne bayan tattaunawa da abokan hulɗa na Saudiyya da kuma shugabannin Hukomomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, wanda hakan ya samar da ragin fiye da Naira 200,000 ga kowanne mahajjaci daga cikin kujeru 66,910 da aka ware wa Najeriya.
“Wannan nasara ba wai a baki ba ce kawai, illa kuwa sakamakon gaskiya ne. Wannan ya yi daidai da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ‘Sabon Fata’, wadanda ke nufin rage nauyi ga al’umma,” in ji shugaban NAHCON.
Ya ƙara da cewa, baya ga wannan rangwame, tafiyar ta samar da ginshiƙi mai ƙarfi ga aikin Hajjin 2026, inda aka riga aka sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama.
Shugaban ya kuma bayyana cewa NAHCON ta gudanar da tattaunawa kai tsaye da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, inda suka ɗauki darussa daga aikin Hajjin 2025 don gabatar da shawarwari masu ƙarfi domin inganta ayyuka.
Haka kuma, ya sanar da ƙaddamar da Kwamitin Tantance Kamfanonin jigilar alhazai masu zaman kan su na Hajjin 2026, inda ya ce kawai kamfanonin da suka cika ka’idoji za a ba damar hidimtawa mahajjatan Najeriya.