
DA DUMI DUMI: Dan majalisar Amurka Maisuna Scott Perry yace Duk Mutanen da Yan B0K0 H$ram Suke kashewa a Nigeria Ƙasar Amurka ce take ɗaukar Nauyi, ƙasar Amurka ce ke daukar nauyin kungiyoyin dake ayyukan halaka al’umma a Nigeria.
Dan majalisar Amurka Maisuna Scott Perry ya bayyana cewa Amurka ce ke daukar nauyin kungiyoyin dake ayyukan halaka al’umma a Nigeria…
Dan majalisar yana wannan jawabin ne a ranar 13 ga watan Fabrairu na wannan shekarar lokacin da ake tattaunawa a zauren majalisar akan ayyukan hukumar USAID wacce gwamnatin Amurka ke daukar nauyin ayyukanta…
Scott Perry yayi jawabi akan tarin hujjojin da suka tattara wadanda suke nuna yadda hukumar USAID take bawa kungiyoyin tada zaune tsaye kudade da makamai duk saboda su halaka mutane a Nigeria …
Idan mun dawo kan jawabin da shugaba Trump yayi a wannan rana, inda yake bayyana Nigeria a matsayin kasar dake halaka kiristoci, hakan na nufin kenan ita amurkan ce ke aikata ayyukan halaka kiristoci a Nigeria tunda sune suke da alhakin duk ayyukan kungiyoyi masu kashe kashe a Nigeria.