gallery edit 1763750262060

DSS ta ɗauke Kanu zuwa gidan yari na Sakkwato

Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) ta mayar da shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, Mazi Nnamdi Kanu, zuwa Cibiyar Kula da Fursunoni ta Najeriya da ke Sakkwato.

Wannan ya biyo bayan hukuncin da aka yanke masa na laifin ta’addanci.

Yayin da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ce hukumar DSS tana da ikon mayar da Kanu zuwa kowace cibiyar gyaran hali a faɗin ƙasar.

A ranar Jumu’a, lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya tabbatar da mayar da Kanu Sokoto.

Ya rubuta cewa: “An sauya wa Mazi Nnamdi Kanu wyri daga DSS Abuja zuwa gidan gyaran hali (prison) na Sokoto; nesa da lauyoyinsa, danginsa, masoyansa da masu yi masa fatan alheri.”

Wata majiya ta tabbatar wa Daily Trust cewa an mayar da Kanu zuwa Sokoto da gaske.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version