
Daga Ibrahim Ammani
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar, ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar ƙaramar hukumar Funtuwa Honorabul Abubakar Muhammad Total, ya bayyana dalilan da yasa ya ɗauki matakin sayawa jama’ar mazaɓar shi Bindigogi.
Da yake zantawa da wakilnmu a Katsina, Honorabul Abubakar Total ya bayyana cewar tura ce takai bango na yadda ‘yan bindiga ke kai hare haren ta’addanci a yankin, wanda hakan ya tursashi ɗaukar sayen bindigogin domin jama’a su kare kansu
“A wata ziyara da na kai yankin Bagari da Unguwar Shanu da Nasarawan Maska, inda hare haren suka fi ƙamari domin a wani hari da ‘yan bindigar suka kai yankin sun kwashi mutane babu adadi inda jama’ar yankin suka yi kukan kura su kabi ‘yan bindigar da duwatsu, ka ga abin ba zai yiwu ba mutum na ɗauke da AK 47 kai kana bin shi da dutse, to sai jama’ar suka shigar mini da buƙatar na saya musu bindigogi domin kare kai, ni kuma a matsayina na wakili na ɗauki matakan da suka kamata na sayo bindigogin sannan na damƙa su a hannun jami’an tsaro na (Community Watch) domin horar da jama’ar “
Ɗan Majalisar ya ƙara da cewar halin da jihar Katsina ta tsinci kanta yanzu a ciki ya zama dole ayi dukkanin mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan fitina ta ‘yan bindiga wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa
Sai dai dan majalisar ya yaba da ƙoƙarin Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda na samar da jami’an tsaron na Community Watch, inda yace da ba don wannan kokari na gwamnan ba da jihar Katsina ta gagari kowa zama.
“Matsalar tsaro da muke fuskanta ya samo asali ne na rashin bada wuka da nama da gwamnoni, inda zai zamana za a samar da ‘yan Sandan Jihohi masu amsar umarni kai tsaye daga Gwamna babu shakka matsalar rashin tsaro za ta zama tarihi a arewa, domin halin da ake ciki yanzu jami’an tsaro na gwamnatin tarayya sun yi ƙaranci sosai ‘
Honorablul Abubakar Muhammad Total ya yi kira ga shugabannin tsaro gaba ɗaya da cewar su ƙara ƙaimi bisa kan wanda suke dashi domin tunkarar ‘yan ta’adda da murƙushe su gaba ɗaya.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko abknaisa100@yahoo.com