Screenshot 20251117 120947

Da dumi’dumi: Babu wanda ya yi yunkurin kisan AM Yerima a Abuja ‘yan sanda ne kawai suka tare shi -Wike

Ta bakin Hadimin sa Ministan FCT, Lere Olayinka, ya ce ba wani yunkurin kisa aka yi wa Lt. A.M. Yarima ba kamar yadda ake ta yada wa a shafukan sada zumunta.

A cewarsa, jami’in na Navy yana tuka mota mai duhun gilashi ba tare da lamba ba, abin da ya sa ‘yan sanda suka tsayar da shi domin tantance ko wanene.

Sai dai ya ce, Yarima ya ƙi bayyana kansa, ya kuma zagi jami’an da ke bakin aiki, wanda hakan ya haddasa ce-ce-ku-ce har aka ɗauki hotunan bidiyon da suka bazu a kafafen sada zumunta.

Olayinka ya jaddada cewa, “Babu wani shirin kisa. Rigimar ce kawai tsakanin jami’in Navy da ‘yan sanda kan ƙa’idar tuki a Abuja.”

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version